Yadda hackers suke hacking social media account
Yawanci hac-king na waya yafi faruwa a lokacin da aka turo maka Link kabi wannan Link ɗin kashiga cikinsa da zaran ya buɗe a wayarka zaiyi maka Installing na wata software mai leƙen asiri ko kuma wacce zata ƙwace iko da wayar naka, wannan dabarar itace aka kira da Phishing shi kuma wannan Link ɗin ana kiran shi da malicious link, sannan sau tari sukan ɗora irin waɗannan Softwares a jikin wani Documents da zakayi downloading a Internet a sources ɗin da bakada garanti da ingancinsu.
Hanyoyin da suke bi wurin tura Phishing Link akwai ta Email Address ko Text Message da kuma ta Social Media.
Abu na biyu ana Hac-king na wayoyin mu a Lokacin da muka buɗe Wifi namu muna shan data na wani, a wannan Lokacin Hac-kers suna kutsowa, sannan yawan barin Bluetooth a buɗe ko kuma yin Pairing na wani bluetooth ɗin da baka sani ba shima ana shiga tashi ayi Hac-king waya, amma wannan yana kasancewa ne musamman idan akwai masu targeting naka.
Hanya ta ukku itace SIM swap attack idan wani yayi amfani da yardar dake tsakaninku zai iya zuwa yayi amfani da details naka yayi swapping layinka wanda hakan zai bashi damar ya samu wasu Information naka da samun damar recieving kiran wayar da za'a maka da text messages, sannan zai samu full access da account naka na banki zai iya kwashe ko nawa ne ka zuba a ciki.
Hanya ta biyar itace ake kira da "Trojan horse malware" irin wannan hanyar ce zakaje ɗauko wata Application wacce zakaganta a ido kamar dagaske amma a zahirance cike take da malicious code da aka ƙirƙire su domin ayi Hac-king wayar naka ko kuma a saci Information naka, dan haka dole ka kula sosai wurin sauke Apps a wayarka musamman waɗanda bakada tabbaci akansu.
Allah Yataimaka..????
Credit: AREWA TRENDING
@everyone
SIRRIN ANDROID